in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwararrun Britaniya za su fara bincike kan akwatunan nadar bayanai na jirgin saman MH17
2014-07-24 16:00:33 cri

Kwararrun da ke kula da hadarin jiragen sama na kasar Birtaniya, za su fara aikin bincike kan dalilan faduwar jirgin saman kasar Malaysia mai lamba MH17 daga na'urorin nadar bayanan jirgin guda 2, da tuni aka mika su hannun wakilan kasar Malaysia a Ukraine, kafin mika su zuwa kasar Birtaniya a ranar 23 ga watan nan na Yuli.

Hukumar bincike kan hadarin jiragen sama ta kasar Birtaniya, ta tabbatar da cewa, ta riga ta karbi akwatunan nadar bayanai guda 2, na jirgin saman nan MH17 da ya fado a kwanakin baya. An kuma mika su ga hedkwatarta da ke gundumar Hampshire.

Bisa bukatar kasar Holand, an ce kwararrun za su fitar da bayanan da ke cikin akwatunan, kafin daga bisani kwararrun kasashen Holand da Britaniya su yi nazari a kansu.

Kakakin ma'aikatar sufuri ta Britaniya da ke shugabantar hukumar nan ta binciken hadarin jiragen sama ya yi nuni da cewa, kwararrun hukumar za su gaggauta kididdigar da za su yi, kafin a rasa damar tantance bayanan da ke cikin akwatunan, sa'an nan kuma za mu bayyana sakamakon da suka samu ga hukumomin bincike na kasashen duniya. Matakin da suke da yakinin nasarar sa.

Bisa labarin da muka samu, an ce, idan har ba a lalata akwatunan ba, kwararru za su iya tantance bayanan dake ciki, nan da awoyi 24 masu zuwa. Koda yake hakan zai zama aikin ne na farko da za a yi wajen binciken lamarin, duba da cewa mai yiwuwa ne a shafe lokaci mai tsaho, makonni ko ma fiye da shekara wajen wannan aiki kafin kaiwa ga karshen sa.

Duk dai da matakan da ake dauka yanzu haka, wasu kwararru su na nuna shakku kan cimma nasarar wannan bincike. A cewar tsohon shugaban hadaddiyar kungiyar zirga-zirgar jiragen sama ta kasar Britaniya Stewart John, kididdigar da za a yi ba ta da amfani ko kadan, duba da cewa wannan faduwa da jirgin na MH 17 ya yi ba irin wadda aka saba gani yau da kullum ba ce.

John ya ce akwatunan za su iya samar da bayanai masu amfani ne kawai, idan har jirgin ya fado sakamakon matsalar fasahohi, amma tun da jirgin sama na Malaysia ya fado ne sakamakon fashewa, wadannan na'urorin sun daina aiki. Don haka a cewar John ana iya ganin cewa, kididdigar da kwararrun za su iya samu daga jirgin ba ta wuce irin wadda ake tattarawa a yau da kullum ba a yayin tafiye-tafiye.

Game da wasu labarai da ke nuna cewa, mai yiwuwa ne an sauya yanayin wadannan akwatuna, wani manazarci kan harkokin tsaron zirga-zirgar jiragen sama a Jami'ar Loughborough na kasar Britaniya Mista David Gleave, ya ce cikin dan lokaci da aka shafe kafin mika akwatunan ga wakilan kasar Malaysia, ba zai yiwu a sauya yanayin su ba.

Wasu kamfanonin watsa labarun kasar Britaniya dai sun yi hasashen cewa, ko da yake akwai yiyuwar canza sashen ajiyar bayani, ko amfani da wata manhaja don yin gyara kan akwatunan bayanan, a hannu guda yawan bayanan kididdigar da akwatunan suke dauke da su sun kai 80, wanda ke nuna cewa idan har lambobin katin ajiyar bayanan sun dace da akwatunan, to ko shakka ba bu ba za a iya canza, ko gyara kididdigar dake cikin akwatunan ba. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China