in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
EU ta yi barazanar kara sanya wa Rasha takunkumi
2014-07-23 15:42:26 cri

Yau Laraba 23 ga wata, kasar Malaysia ta ce, za a kai akwatunan nadar bayanai biyu na jirgin saman Malaysia MH17 kasar Birtaniya domin yin musu nazari

A wannan rana, Liow Tiong Lai, ministan sufuri na Malaysia ya yi bayani a cikin wata sanarwa da cewa, tawagar kasa da kasa karkashin shugabancin kasar Holland ta tsai da kudurin mika akwatunan 2 a hannun hukumar bin bahasin hadarurrukan jiragen sama ta Birtaniya domin yin musu nazari.

Ranar 22 ga wata, ministocin harkokin wajen kasashe mambobin kungiyar tarayyar Turai EU sun yi taro a birnin Brussels, inda suka yi kira da a bi bahasin hadarin jirgin saman cikin adalci da 'yanci, sun kuma kalubalanci kasar Rasha da ta ba da nata tasiri kan dakarun da ke gabashin kasar Ukraine a fannonin daidaita batutuwan da suka biyo bayan hadarin jirgin da yadda ake bin bahasin hadarin. Sun kuma bukaci Rasha da ta daina bai wa dakarun makamai, dole ne ta hana su shiga iyakokin kasa. Har wa yau kudurin ya ce, idan Rasha ba ta biya wadannan bukatu ba, sai kungiyar za ta kara sanya mata takunkumi.

Dangane da haka, Vladimir Chischov, jakadan Rasha a kungiyar EU ya ce, kasarsa na fatan sassa daban daban ba za su sanya siyasa cikin hadarin jirgin saman ba, sanya wa Rasha takunkumi ta fuskar tattalin arziki ba shi da amfani. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China