in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin ya nuna alhini ga rasuwar mutanen da dama a hadarin jirgin saman MH17
2014-07-24 10:36:41 cri
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Liu Zhenmin, ya ziyarci ofishin jadakancin kasar Malaysia dake nan kasar Sin a jiya Laraba, domin nuna alhinin rasuwar mutane da dama sakamakon hadarin jirgin sama nan na kasar Malaysia mai lamba MH17.

A zantawarsa da jakadan kasar Malaysia dake nan kasar Sin, Mr. Liu ya ce gwamnatin kasar Sin, da jama'arta na jimamin hadarin jirgin na MH17, suna kuma nuna goyon bayansu ga yunkurin da kasashen duniya ke yi game da gudanar da bincike kan musabbabin fadowar jirgin cikin adalci.

Ya ce kamata ya yi hukumar jiragen sama na kasa da kasa, ta taka muhimmiyar rawa kan wannan batu. A cewar Mr. Liu, kasashen Sin da Malaysia makwabtan juna ne da ke da dadadden zumunci, don haka Sin ke fatan ci gaba da goyawa kasar Malaysia baya, tare da ba ta dukkanin tallafin da ya wajaba.

Da ya ke maida jawabi, jakadan kasar Malaysia a nan kasar Sin Mr. Iskandar Sarudin ya ce, kasarsa na da aniyar hadin gwiwa tare da kasashen duniya ciki har da kasar Sin, wajen tabbatar bincike kan dalilin aukuwar hadarin cikin adalci. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China