in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ra'ayin kasar Sin game da kudurin MDD kan hadarin jirgin sama na MH17
2014-07-22 10:55:12 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei, ya bayyana cewa, kasar Sin na da imanin cewa, za a iya aiwatar da kudurin da kwamitin sulhu na MDD ya zartas, kan binciken dalilin aukuwar hadarin jirgin saman nan na kasar Malaysia mai lamba MH17. Kana kasar na sake yin kira ga bangarori daban daban da wannan batu ya shafa, da su bada tallafin hadin kansu domin nasarar aikin binciken hadarin, a kokarin gano ainihin dalilin na aukuwarsa cikin hanzari.

Hong Lei, wanda ya amsa tambayoyin manema labaru kan wannan batu yau Talata 22 ga wata, ya furta cewa, a safiyar yau bisa agogon Beijing, kwamitin sulhu na MDD ya zartas da kuduri mai lamba 2166, kan batun faduwar jirgin saman na MH 17 a gabashin kasar Ukraine, inda kasar Sin ta jefa kuri'ar amincewa da kudurin.

Hong ya kara da cewa, kasar Sin ta yi bakin ciki da abkuwar hadarin, ta kuma sake bayyana ta'aziyya ga wadanda wannan lamari ya shafa, da kuma dukkanin wadanda suka rasa iyalansu yayin hadarin.

Bugu da kari, kasar Sin na goyon bayan aikin binciken musabbabin faduwar wannan jirgi cikin 'yanci da adalci, ta kuma yi kira ga kungiyar jiragen saman fasinja ta kasa da kasa, da ta taka muhimmiyar rawa wajen wannan bincike.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China