in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An baiwa kasar Malaysia akwatin nadar bayanan jirgin sama na MH17
2014-07-22 20:42:26 cri
Firaministan kasar Malaysia Najib Tun Razak ya sanar da cewa shugaban 'yan tawaye dake gabashin Ukraine Alexander Borodai ya mika wa kasar akwatin nadar bayanan jirgin sama na MH17 da ya fadi a wannan yankin.

A lokacin taron manema labarai da aka shirya a safiyar wannan rana ta talata 22 ga wata,Firaministan ya ce yanzu haka an riga an kulla yarjeniyoyi uku da shugaban 'yan tawayen Alexander Borodai wanda har ila yau shi ne firaministan jamhurriyar Donetsk kan yadda za a daidaita wasu ayyuka bayan faduwar jirgin sama na MH17.

Mr Najib ya tabbatar a wannan rana na talata cewa, da farko bangarorin biyu sun amince da sufurin gawawaki 282 da aka ajiye a jihar Donetsk zuwa birnin Kharkiv da jirgin kasa, daga baya kuma za a mikawa wakilan kasar Holland wadannan gawawaki.

Yarjejeniya ta biyu kuwa, bangarorin biyu sun amince da mikawa kasar Malaysia akwatunan nadar bayanan jirgin sama biyu. Bisa yarjejeniyar da bangarorin biyu suka daddale,wanda daga bisani Malaysia zata mikawa masanan hukumar zirga-zirgar jiragen sama. Sai na uku inda ya ce mambobi masu kula da aikin nazari na kasa da kasa za su sami iznin shiga wurin da jirgin ya fadi, kuma za su yi bincike kan wannan hadari yadda ya kamata. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China