in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu ya kalubalanci sassa daban daban da su ba da taimako ga binciken dalilin hadarin jirgin saman Malaysia MH17
2014-07-22 16:07:10 cri

A ranar Litinin 21 ga watan nan ne kasashe mambobin kwamitin sulhu na MDD, suka kada kuri'a kan wani sabon kuduri da kasar Australia ta gabatar, kudurin da ya samu amincewar mambobin kwamitin 15, wanda kuma ya kunshi nuna matukar damuwa da jimani game da hadarin jirgin saman kasar Malashiya mai lamba MH17.

Kudurin ya kuma goyi bayan a gudanar da binciken dukkanin dalilin aukuwar hadarin cikin 'yanci daga dukkan fannoni, bisa ka'idojin jiragen saman fasinja na kasa da kasa. Sa'an nan kudurin ya bukaci a girmama, tare da tattara gawawwakin wadanda suka rasa rayukansu sakamakon hadarin yadda ya kamata.

Kaza lika kudurin ya kuma bukaci dakarun da ke iko da wurin da jirgin ya fadi, da su samar da kyakkyawan yanayi, tare da tabbatar da tsaron ma'aikatan bincike, da ba su damar gudanar da binciken ba tare da gindaya wani sharadi ba. Kudurin ya kuma bukaci a dakatar da daukar dukkan matakan soja a kewayen wurin, domin gudanar da binciken ba tare da wata matsala ba.

Har wa yau an bukaci a gurfanar da wadanda suke da hannu kan aukuwar hadarin a gaban kotu, matakin da kuma dukkan kasashen za su ba da taimako game da shi.

Jim kadan da jefa kuri'ar, zaunanniyar wakiliyar kasar Amurka a MDD Samantha Power, ta ce kasar Rasha ta amince da kudurin a wannan rana, kana Amurka ma ta yi maraba da hakan. Koda yake ta ce da kasar Rasha ta yi amfani da tasirinta kan 'yan-a-waren dake yankin da hadarin ya auku, wajen sanya su kwance damara, da mika yankin hannun kwararru na kasa da kasa, da ba a bukaci batun jefa kuri'ar ba.

Dangane da wannan tsokaci na Power, zaunannen wakilin Rasha a MDDr Vitaly Churki, ya ce wancan tsokaci na wakiliyar Amurka ba shi da nasaba da batun da ake yi, don haka kamata ya yi a koma tattaunawa kan yadda za a gano dalilin aukuwar hadarin yadda ya kamata.

A daya bangaren kuma da sanyin safiyar ranar Talata 22 ga wata, firaministan Malaysia Najib Tun Razak, ya ce shi da shugaban dakarun gabashin kasar Ukraine Alexander Borodai, sun cimma matsaya daya, dangane da mika gawawwakin wadanda suka mutu cikin hadarin a hannun wakilan kasar Holland, tare da mika akwatunan nadar bayanan jirgin saman a hannun kwararrun Malaysia, sun kuma yarda da kwararrun kasa da kasa su shiga wurin da jirgin ya fadi domin aikin bin bahasi daga dukkan fannoni.

Bisa kuma wani labarin da kamfanin dillancin labaru na Interfax ya fitar a ranar 22 ga wata, an ce, a safiyar wannan rana, Borodai ya mika akwatunan 2 a hannun mahukuntan Malaysia.

Haka zalika, shugaban Ukaine Petro Poroshenko, ya umurci sojojin gwamnatin da su tsagaita bude wuta a yankin da ke da'irar kilomita 40 tsakaninsu da wurin da jirgin ya fadi. Bugu da kari, firaministan Ukraine Arseniy Yatsenyuk, ya tabbatar da cewa, a ranar 21 ga wata, kwararru daga tawagar kasa da kasa karkashin rukuni na farko, dake bin bahasin hadarin jirgin saman, sun isa birnin Kharkiv da ke gabashin kasar, kana gwamantin kasar za ta baiwa wadannan kwararru 30 daga kasashen Holland, da Amurka, da Jamus da dai sauransu taimako wajen shiga wurin da hadarin ya auku, kasancewar hakan zai bada kafar samar da jin kai.

A dai wannan rana ta 21 ga wata, ma'aikatar tsaron Rasha ta kira wani taron manema labaru kan hadarin jirgin saman na MH17, inda ta gabatar da wasu bayanan sa ido da rundunar sojan Rasha ta samu. Ta kuma bayyana cewa, kafin jirgin saman ya isa Donetsk, yana bin hanya da tsarin farko, amma daga bisani ya juya zuwa arewa, ya dan sauya hanyar da ya bi, bai kuma koma hanyar da ya tsara bi a baya ba.

Ma'aikatar tsaron Rasha na ganin cewa, ba za a iya gano dalilin da ya sa jirgin ya kauce hanyarsa ba, sai an yi nazari kan bayanan da ke cikin akwatunan nadar bayanan jirgin saman.

Har wa yau a ranar ta Litinin, shugaba Barack Obama na Amurka ya sake yin kira da a bi bahasin hadarin jirgin daga dukkan fannoni, ba kuma tare da wani tarnaki ba.

Shi kuwa firaministan Birtaniya Sa'an nan David Cameron, cewa ya yi idan Rasha ba ta canza ra'ayinta kan hadarin ba, kasarsa za ta sa kaimi ga kungiyar tarayyar Turai, da ta kara sanya mata takunkumi.

Shi kuwa firaministan Holland Mark Rutte, cewa ya yi ya zama tilas gwamnatinsa ta gano tare da dawo da dukkan gawawwakin wadanda suka mutu cikin hadarin jirgin ba tare da bata lokaci ba. Rutto ya kuma jaddada cewa, tilas ne Rasha ta tirsasa 'yan-a-waren da ke gabashin Ukraine, su kyautata halin da ake ciki a wurin da jirgin ya fadi, domin bada damar bin bahasin hadarin yadda ya kamata. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China