in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fadada wuraren da ake neman abubuwan dake cikin jirgin saman MH17
2014-07-21 10:06:18 cri

Ofishin watsa labaru na hukumar kula da halin dokar ta baci ta kasar Ukraine ya bayar da wata sanarwa a ranar 20 ga wata cewa, an fadada wurin gudanar da bincike a filin da jirgin saman MH17 na kasar Malaysia ya fadi da muraba'in kilomita 50 a jihar Donetsk, ciki har da sake bincike kan wuraren da suka kai fadin muraba'in kilomita 32 da aka yi bincike a kwanakin baya.

Sanarwar ta bayyana cewa, hukumar ta dauki nauyin daidaita ayyukan gudanar da bincike da bada ceto, yanzu mutane 800 ne suka shiga ayyukan.

Jirgin saman MH17 na kasar Malaysia ya fadi a yankin gabashin kasar Ukraine dake dab da iyaka da kasar Rasha a ranar 17 ga wata, inda dukkan fasinjoji da ma'aikata 298 dake cikin jirgin suka rasa rayukansu. Wurin da jirgin ya fadi na karkashin ikon 'yan tawayen kasar Ukraine ne. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China