in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kafa tawagar hadin gwiwar bincike kan hadarin jirgin saman MH17
2014-07-21 15:11:17 cri

Ministan harkokin sufuri na kasar Malaysia Liow Tiong Lai, ya bayar da wata sanarwar dake cewa, an kafa tawagar hadin gwiwa ta kasa da kasa, wadda za ta bi habasin hadarin jirgin saman kasar Malaysian nan mai lamba MH17. Sanarwar ta ce tawagar ta kunshi jami'an kasashen Holland da Malaysia, da wakilan cibiyar binciken hadarorin jiragen sama ta kasar Birtaniya, gami da jami'an kwamitin kiyaye zaman lafiya ta fuskar sufuri ta kasar Amurka.

Mr. Liow ya fadi hakan ne a jiya Lahadi a birnin Kiev na kasar Ukraine. Yana mai cewa, gwamnatin kasar Ukraine ta riga ta sanar da wannan tawagar bincike, cewar wurin da wannan jirgi ya fadi yana hannun dakarun sa kai na kasar, don haka gwamnatin ba ta iya ba da tabbaci ga wakilan tawagar wajen kiyaye lafiyarsu a wurin ba.

Ya zuwa yanzu dai, kungiyar tsaro da hadin gwiwa ta Turai ita ce kungiyar kasa da kasa daya tak, da ta shiga wurin da jirgin ya fadi cikin gajeren lokaci.

Bugu da kari, Mr. Loiw ya ce, kasar Malaysia na kulawa sosai game da batun hana masu bincike shiga wurin da hadarin ya auku. Kaza lika Liow na ganin cewa, abin da ya fi dacewa a gaggauta aiwatarwa yanzu haka shi ne, tabbatar da masu bincike na kasa da kasa, da masu aikin ceto sun shiga wurin da jirgin saman ya fadi, ba tare da wani cikas ba.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China