Kakakin sojojin Isra'ila Peter Lerner ya bayyana a wannan rana cewa, matakan da sojojin kasarsa suke dauka na kare kai ne, ba a bada umurnin kai hari ta kasa a zirin Gaza ba, suna kai hari ta sama ne kawai. Lerner ya kara da cewa, don tinkarar harin makaman roka daga zirin Gaza, sojojin kasar Isra'ila za su kara fafatawa da dakaru a zirin. Idan har ba su dakatar da kai hari da makaman roka ba, sojojin za su kara daukar matakan soja a zirin na Gaza.
Game da halin da ake ciki a tsakanin Palesdinu da Isra'ila, shugaban Palesdinu Abbas ya yi kira ga Isra'ila da ta dakatar da ayyukan soja a zirin Gaza cikin hanzari. Abbas ya yi kashedi ga Isra'ila kan mummunan sakamakon da zai iya biyo baya idan rikicin ya tsananta. Kana ya yi kira ga kasa da kasa da su dauki matakai don hana sojojin Isra'ila kawo tashe-tashen hankali a zirin na Gaza. Sai dai Abbas ya kara da cewa, Palesdinu tana yin mu'amala tare da kasashen Larabawa da hukumomin kasa da kasa don sa kaimi ga Isra'ila da ta tsagaita bude wuta. (Zainab)