A ranar talata Babban magatakardan MDD Ban Ki-Moon ya yi suka game da kashe wasu matasa Palesdinawa a birnin Kudus a wannan rana, a sa'i daya kuma ya bukaci bangarorin da abin ya shafa da su kai zuciya nesa su kauce wa tada hankali.
A cikin sanarwar da kakakinsa ya fitar, an ce, Ban Ki-Moon ya jajenta ma iyalan matasan da aka kashe, tare da yin kira da a gurfanar da masu laifuffuka a gaban kotu ba tare da bata lokaci ba.
Mr Ban Ki-Moon ya sake yin kiran ga bangarorin da abin ya shafa da su tabbatar da cewa, ba za su kara tada hankula ba, domin kada hakan ya sake jawo asarar rayuka ko jikata jama'a.
A wannan rana har ila yau, gwamnatin kasar Palesdinu ta yi suka kan kisan gillar da aka yi wa matasan Palesdinawa. A cikin wata gajeruwar sanarwa da ta fitar, shugaba Mahmoud Abbas ya bukaci gwamnatin Isra'ila da ta dauki cikakkun matakai cikin lokaci, don gurfanar da masu laifin a gaban kotu, da kuma hana masu tsattsauran ra'ayi na gani-kashe-ni na matsugunan Yahudawa kai hari ga Palesdinawa, a kokarin kawar da hali mai tsanani da Palesdinu da Isra'ila ke ciki sakamakon tashin hankalin da ya barke.
A daidai wannan ranar kuma, kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas da ke da iko da zirin Gaza ita ma ta yi tir a kan lamarin. (Danladi)