Har yanzu ana fuskantar bambance-fuskance a tsakanin kasashen 6 da kasar Iran kan wasu muhimman batutuwa, ciki har da batun tace Uranium, amma dukkansu sun bayyana cewa, za su yi namijin kokarinsu na kawo karshen shawarwari daga dukkan fannoni kafin 20 ga watan, wato karshen wa'din da aka tabbatar kan shawarwarin.
Mr. Wang Qun, wakilin kasar Sin, kuma direktan hukumar kwace damara ta ma'aikatar harkokin wajen kasar a ran 3 ga wata ya gaya wa kafofin yada labaru cewa, tun daga ranar 2 ga wata, an yi shawarwari tinjim a tsakanin bangarori biyu ko a tsakanin bangarori da yawa cikin kyakkyawan yanayi. Kowane bangare na fatan za a iya daddale wata yarjejeniya tsakaninsu tun da wuri. Ya kuma kara da cewa, ya kamata kowane bangaren ya kara yin kokari. Bangaren Sin a shirye yake wajen yin nasa kokari na daddale wata yarjejeniyar da za ta shafi dukkan fannoni nan da nan.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, tun daga karshen wannan mako, za a fara yin shawarwari tsakanin masana kan batutuwan fasaha. Bisa shirin da aka tsara, ya kamata a kawo karshen wannan shawarwari kafin ran 20 ga watan. (Sanusi Chen)