Manyan kasashe 6 da batun nukiliya na kasar Iran ya shafa, da kungiyar kasashen Turai EU, da kasar Iran, sun yi shawarwari a zagaye na 4 a birnin Viena na kasar Austria don tsara wani kundin yarjejeniya da zai shafi dukkan fannonin wannan batun.
Game da lamarin, mista Hong Lei ya ce, hakan na nufin shawarwarin ya fara tabo wasu abubuwa masu muhimmanci da sarkakiya, don haka za a iya gamuwa da wasu matsaloli, amma dukkan bangarorin da batun ya shafa sun nuna niyyar neman cimma matsaya daya nan da nan. Don haka kasar Sin na fatan ganin an ci gaba da tattaunawa cikin daidaituwa, da kulawa da bukatun kowane bangare, ta yadda za a iya cimma wata yarjejeniyar da ta shafi fannoni daban daban a niyyar da ka nuna. A nata bangaren, kasar Sin za ta ci gaba da kokarin sa kaimi ga wannan aiki, in ji kakakin kasar Sin. (Bello Wang)