in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gabatar da shawarwari biyar don raya dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen Latin Amurka da Caribbean
2014-07-18 10:56:05 cri

An gudanar da taron shugabannin kasar Sin da kasashen Latin Amurka da Caribbean a ranar Alhamis 17 ga wata a birnin Brasilia dake kasar Brazil. Shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugabannin sauran kasashen dake halartar taron sun tsai da kudurin kafa dangantakar abokantaka a tsakaninsu mai adalci da samun moriyar juna har da bunkasuwa tare, sannan a karshe suka sanar da kafa dandalin tattaunawa a tsakaninsu.

A cikin jawabinsa wajen taron, shugaba Xi Jinping ya sanar da matakan da kasar Sin ta gabatar wajen sa kaimi ga hadin gwiwa a tsakaninta da kasashen Latin Amurka da Caribbean. A jawabin nashi mai teken "yi kokarin kafa tsarin bai daya na samun bunkasuwa tare", ya gabatar da shawawari biyar da suka hada da samun fahimtar juna a fannin siyasa, hadin gwiwa a tsakaninsu a fannonin tattalin arziki da cinikayya don moriyar juna, koyar da juna a fannin al'adu, inganta hadin kai kan harkokin kasa da kasa, gami da kyautata dangantaka a tsakanin bangarorin biyu, a kokarin kafa tsarin bai daya na samun bunkasuwa tare.

Ita ma shugabar kasar Brazil Dilma Rousseff ta bayyana godiyarta ga shugaba Xi Jinping da ya gabatar da muhimman shawarwari, kuma ta yi alkawarin cewa, kasashen Latin Amurka da Caribbean za su yi kokari tare da kasar Sin wajen aiwatar da wadannan shawarwarin tare da kafa dandalin tattaunawa don samun bunkasuwa da wadata tare. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China