in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya yi jawabi a majalisar dokokin kasar Brazil
2014-07-17 10:03:48 cri

A ranar 16 ga wata, shugaban kasar Sin Mista Xi Jinping, wanda yake ziyarar aiki a Brazil, ya yi jawabi a majalisar dokokin kasar, inda Xi ya jaddada cewa, za a nuna hangen nesa da bude ido cikin imani don inganta dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu irin ta manyan tsare-tsare a dukkan fannoni, da sa kaimi ga gudanar da tsarin kasa da kasa yadda ya kamata.

Xi a jawabin nasa mai taken "a inganta dangantaka da abokantaka ta gargajiya, da kara hadin kai a tsakanin juna" ya ce, kasar Brazil ta zama kasa ta farko da ta kulla dangantakar abokantaka da kasar Sin a dukkan fannoni bisa manyan tsare-tsare, a matsayinta ta wata kasa mai tasowa da kuma wata kasar da ke nahiyar Latin Amurka. Don haka kasashen biyu sun mayar da juna a matsayin muhimman abokan hadin kai, abin da ya zama wani abin koyi na hadin kai tsakanin kasashe masu tasowa.

Xi ya jaddada cewa, a matsayinsu iri daya na manyan kasashe masu tasowa da ke ba da babban tasiri ga duniya da kuma kasashe masu saurin ci gaba, dangantakar da ke tsakaninsu ta kara takawa muhimmiyar rawa ga duniya.

Ya ce, ya kamata a yi amfani da wannan kyakkyawar dama ta cikon shekaru 40 da kulla huldar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu wajen ci gaba da raya dangantakarsu.

A cikin jawabin na Shugaba Xi, ya gabatar da shawarwari guda uku, da suka hada da tabbatar da alkiblar hadin kan kasashen biyu don zurfafa amincewa a tsakaninsu, sa'anan sai dukufa wajen samun bunkasuwa tare, baya ga sauke nauyin duniya da ke bisa wuyan kasashen biyu, a kokarin kiyaye adalci a duk fadin duniya. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China