Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya sauka kasar Brazil domin halartar taron shuwagabannin kungiyar kasashe da arzikinsu ke saurin bunkasar ta BRICS.
Jim kadan da isarsa, shugaba Xi ya bayyana cewa, kungiyar ta BRICS na da matukar muhimmanci ta fuskar habakar dangantakar kasa da kasa, a sa'i daya kuma tana tallafawa wajen aiwatar da manufofin kasa da kasa.
Shugaba Xi ya kara da cewa, kasarsa na goyon bayan duk wani mataki na hadin gwiwa da ragowar kasashe mambobin kungiyar. Ya ce, a yanzu haka farfadowar tattalin arzikin duniya na fuskantar kalubale da dama, don haka ya bayyana fatansa na ganin an zurfafa tattaunawa karkashin wannan taro, tare da daukar matakan bai daya, don ganin an habaka tattalin arziki, ci gaba tare da bunkasar zaman lafiya a duniya baki daya.
Ana dai sa ran shuwagabannin wannan kungiya daga Brazil, da Rasha, da India, da Sin da kuma Afirka ta Kudu za su halarci wannan taro na yini biyu da za a gudanar a Talata da Laraba. (Saminu)