in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A Najeriya an hallaka 'yan Boko Haram sama da 50
2014-07-06 16:20:35 cri
Rundunar sojin Najeriya ta ce ta samu nasarar harbe magoya bayan kungiyar nan ta Boko Haram sama da 50, yayin wata arangama da dakarun ta suka yi da mayakan kungiyar a garin Damboa na jihar Borno. Koda yake dai akwai rahotanni dake cewa adadin mutanen da suka rasu ya haura hakan.

A cewar kakakin rundunar sojin ta Najeriya manjo janar Chris Olukolade, dauki ba dadin na ranar Juma'a, wanda ya biyo bayan yunkurin da 'yan Boko Haram din suka yi, na aukawa barikin soji da kuma wani caji ofis dake Damboa, ya ritsa da rayukan sojoji 6, ciki hadda wani hafsa daya.

Kaza lika Olukolade ya ce sojoji sun samu nasarar kwace wasu motoci masu sulke 4 daga mayakan kungiyar.

Daga dai Arewa maso gabashin Najeriyar, wani dan kunar bakin wake ya hallaka mutane 5, bayan da ya kai hari kan wani masallaci a ranar Juma'a, a cewar wasu jami'an tsaron kasar. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China