Wata sanarwa da kakakin rundunar sojin ta Najeriya manjo janar Chris Olukolade ya fitar, ta bayyana cewa dauki ba dadin na ranar Juma'a, ya biyo bayan yunkurin da 'yan Boko Haram din suka yi ne, na aukawa barikin soji da kuma wani caji ofis dake Damboa, lamarin da ya sabbaba musayar wuta tare da kisan 'yan Boko Haram din su 50, da sojoji 5, tare da wani hafsa daya.(Saminu Alhassan)