Kakakin rundunar sojin kasar Manjo Janar Chris Olukolade wanda ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da kamfanin dillanci labarai na kasar Sin Xinhua ta samu ya ce rundunar sojin kasar sun kawar tare da kwato dajin Balmo a wani samame da suka kai a wanda ya dauki daukacin karshen makon da ya kare.
Ya ce kafin wannan aiki Dajin Balmo wanda ya mika har cikin jihohin Bauchi da Jigawa yana hannun 'yan ta'addan ne inda suka mayar da shi sansani da maboyar su suna kai hare hare a kan al'umma.(Fatimah Jibril)