Wata majiya ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin cewa,mayakan na Boko haram sun sace sarkin Uba Isma'il Mamza da takwaransa na Gwoza Idriss Timta ne da misalin larfe 9 na safe agogon wurin, a kusa da kauyen Zhur da ke kan iyakar Borno da Adamawa.
Bayanai na cewa, sarakunan gargajiyar suna kan hanyarsu ce ta zuwa Gombe don halartar jana'izar marigayi sarkin Gombe.
Wani mazaunin garin na Uba mai suna Ezekiel Buba ya shaidawa Xinhua a garin Maiduguri,babban birnin jihar Bonro cewa,an sanar da al'ummar yankin game da sacen sarkin nasu.
Koda ya ke wata majiyar tsaro ta ce wasu sojoji sun yi nasarar gano sarkin na Uba,kuma suna kokarin ganin an sako shi.
Sai dai babu wani bayani a hukumance daga sojoji ko gwamnatin jihar game da sarakunan da aka sacen.(Ibrahim)