in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen BRICS sun sanar da kafa sabon bankin samar da ci gaba
2014-07-16 16:32:48 cri

Yayin taron tattaunawa na shugabannin kasashen BRICS da aka gudanar a ranar 15 ga wata, ministocin kudi na kasashen BRICS sun sa hannu kan wata yarjejeniyar da ta kunshi kafa sabon Bankin raya kasashen na BRICS a gaban shugabanninsu.

Ministan kudin kasar Sin Mista Lou Jiwei ne ya sa hannu a madadin gwamnatin kasar Sin. Yayin zaman shugaban kasar Sin Mista Xi Jinping ya bayyana cewa,

"Bisa kokarin da bangarori daban daban suka yi, an kai ga cimma matsaya guda kan kafuwar sabon Bankin raya kasashen BRICS, lamarin da ya zama wani kyakkyawan sakamako mai muhimmanci da kasashen BRICS suka samu a yunkurin su na hada kai, matakin da kuma ya bayyana burin siyasa na kasashen, wajen hada kai da samun bunkasuwa tare. Kafuwar wannan banki ba kawai za ta kara karfin kasasahen BRICS a matsayin mai fadi-a-ji a harkokin kudi na duniya ba ne kawai, har ma za ta samar da moriya ga jama'ar kasashe masu tasowa. Ina godiya da goyon bayan da kuka nuna wajen kafa hedkwatar wannan banki a birnin Shanghai, muna fatan yin hadin kai da bangarori daban daban wajen gudanar da aikin share fage, ta yadda za a iya bude bankin cikin sauri."

A dai wannan rana, a madadin gwamnatin kasar Sin, shugaban Bankin jama'ar kasar Sin Mista Zhou Xiaochuan ya sa hannu kan yarjejeniyar kafa asusun tinkarar al'amuran gaggawa na kasashen BRICS.

Game da haka, shugabar kasar Brazil Madam Dilma Rousseff ta yi nuni da cewa,

"A yau mun tabbatar da shirin kafa Bankin raya kasashen BRICS, da kuma asusun tinkarar al'amuran gaggawa na kasashen BRICS, wannan mataki ne da zai zama mai matukar muhimmanci ga aikin kyautata harkokin duniya. Mun riga mun zartas da sanarwa dake nanata cewa, za mu inganta hadin kai a harkokin shiyya-shiyya da na duniya. Matakin da ya shaida cewa, ko da yake kasashen BRICS suna da nisa da juna, da al'adu bambanta, a hannu guda mun dukufa wajen kafa dangantakar abokantaka mai karko, matakin da zai taimaka wajen kyautata tsarin duniya."

A cikin jawabinsa, Mista Xi Jinping ya ce, a daidai wannan lokaci, kamata ya yi kasashen BRICS su tsara wani sabon shiri da zai karfafa kwarewar su a fannin raya tattalin arziki.

"Dole ne mu yi amfani da fasahohin da muka samu a baya, sa'an nan kuma mu tsara wani sabon shiri. A ganina wannan sabon shiri zai karfafa ingancin dangantakar abokantaka a fannoni daban daban a tsakanin kasashen BRICS. Hakan ya nuna bukatar ci gaba da raya dangantakar musamman a tsakaninmu, ya dace mu tsaya tsayin daka wajen bude kofa, da nuna fiffiko da muke da shi, da kara hadin kai a fannin tattalin arziki, da samar da wata babbar kasuwa a duk duniya, da kyautata harkokin tattalin arziki na duniya, da bunkasa tattalin arzikin duniya."

A 'yan shekarun baya, kasashen BRICS sun gudanar da hadin kai a fannonin siyasar duniya, da tattalin arzikin kasa da kasa, da hadin kai kan hakikanan abubuwa, musamman ma fannin samun sulhu kan batutuwan da ke jawo hankalin jama'ar kasashe daban daban dangane da yaki da ta'addanci, da batutuwan da suka shafi Gabas ta Tsakiya, da Afghnistan, da Sham da Ukraine da dai sauransu. Game da haka, Madam Dilma Rousseff ta ce,

"Ta hanyar hadin kanmu, muna da damar waiwayar wasu manyan batutuwan duniya a fannonin tattalin arziki da siyasa, mun tattauna kan yaki a wasu shiyyoyi, da batutuwan da ke jawo hankulan jama'a, musamman halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya, ciki har da matsalolin Sham da Iraki, da rikicin Palesdinu da Isra'ila, da halin da ake ciki a Ukraine. Mun san cewa, mun samu ci gaba dangane da halin da ake ciki a duk duniya, amma dole ne mu bi wata hanyar da ta dace cikin dogon lokaci, ciki har da shawarwari da juna, mun yi kira ga bangarori daban daban da su tattauna da juna, mu kasashen BRICS mun cimma ra'ayi daya cewa, wajen daidata matsalolin da ke janyo hankulan jama'a na shiyyoyi, tilas ne bangarori daban daban na duk duniya su yi kokari cikin hadin gwiwa, ba kawai kasashen da ke da nasaba da batun ba, har ma da daukacin al'ummomin duniya baki daya." (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China