in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen BRICS za su kara tasiri ga duniya, in ji kwararrun kasar Rasha
2014-07-14 16:23:34 cri

A ranar 15 ga watan nan ne ake fatan gudanar da taron koli karo na 6 na rukunin kasashe 5 da tattalin arzikinsu ke saurin bunkasa, ko BRICS a takaice. Kasashen da suka hada da Brazil, da Rasha, da Indiya, da Sin da Afirka ta kudu, taron da zai gudana a birnin Fortaleza na kasar Brazil.

Ana sa ran shugabannin kasashen biyar ciki har da na kasar Sin za su halarci taron, don tattaunawa kan ayyukan da suke da ruwa da tsaki a cikin su. An ce aiki na farko da za a tabbatar a gun taron shi ne, kafa wani bankin raya duniya, wanda da farko za a zubawa jarin dala biliyan 50.

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Mista Li Baodong ya bayyana a gun taron manema labaru da aka shirya a 'yan kwanakin baya cewa, taron kolin na wannan karo zai zama wata kyakkyawar dama da aka samar domin kafuwar bankin raya duniya, kuma kasashen BRICS suna da ra'ayi daya kan batun kafuwarsa. Game da haka, mataimakin darektan hukumar nazarin harkokin Gabas mai nisa Mista Andery Astrowski, ya yi nuni da cewa, kafuwar bankin raya duniya ya zama wani mataki mai muhimmanci ga bunkasuwar kungiyar kasashen BRICS. Ya ce,

"Shugabannin kasashen BRICS su kan yi shawarwari da juna, amma a hakika tasirin da kungiyar take da shi ga duniya kadan ne, idan aka kwatanta shi da na sauran kungiyoyin duniya kamar G8, da Asusun lamuni na duniya IMF, da Bankin Duniya da dai sauransu. Haka nan jimillar tattalin arzikin da kasashen BRICS suke da shi ya yi daidai da na kasashen kungiyar tarayyar kasashen Turai wato EU, don haka a kan yi tambayar ko me ya sa kasashen BRICS ba su da tasiri kamar EU? Amsar dai ba ta wuce saboda kasashen BRICS din ba su da tasirin kudi nasu na kan su, wato ba su da bankinsu na daban.

Don haka dai kafuwar bankin raya duniya zai taimakawa kasashen na BRICS, wajen gudanar da shirin zuba jari a gida, haka kuma ya zama wani mataki mai muhimmanci ga bunkasuwar kasashen kungiyar."

Shi ma wani kwararre a hukumar nazarin tattalin arzikin duniya, da dangantakar da ke tsakanin kasashen duniya a kasar Rasha Mista Vladimir Kondratiev ya ce,

"A ganina, wannan banki yana da wata kyakkyawar makoma, wato kudaden da za a zuba ta cikin sa, za su taimakawa Rasha wajen inganta manyan ayyukan more rayuwar jama'ar ta, kana kasar Sin tana son raya yankin tattalin arziki na siliki, ita ma tana bukatar kudade da yawa, wannan bankin zai iya taimaka musu, baya ga batun jigilar Gas a tsakanin Rasha da Sin, da raya yankunan Kuriyar Arewa, da kuma shirin Brazil, da na Afirka ta kudu, har ma da shirin yada harkar iskar gas na Sin da Rasha har ya zuwa kasar India. Kafuwar bankin raya duniya zai iya bayar da goyon baya a fannin kudi wajen aiwatar da wadannan shirye-shirye."

Game da makomar bunkasuwar kasashen BRICS, Mista Kondratiev ya yi nuni da cewa, yawan jama'a da albarkatu da kasashen na BRICS suke da su sun tabbatar da cewa, kasashen kungiyar na da wata kyakkyawar makoma wajen samun bunkasuwa, a nan gaba, haka nan tasirin wannan kungiya zai wuce na ko wace irin kungiya a duniya.

"Makomar bunkasuwar kasashen BRICS a nan gaba tana da nasaba da yawan jama'ar da suke da su, sabo da suna da jama'a masu yawan gaske, sa'an nan kuma suna da babbar bukata a kasuwa, hakan ya sa tattalin arzikin su zai iya samun bunkasuwa. Kamar yadda muka sani, yawan jama'ar da kasashen BRICS suke da su ya wuce rabin jama'ar dukkanin duniya, sabo da haka a nan gaba kasashen BRICS za su tabbatar da bukatun duniya.

Ban da wannan kuma, kasashen na BRICS suna da arzikin albarkatun kasa masu yawan gaske, ciki har da gas, da man fetur, da ma'adinnan karfe da dai sauransu. Sabanin kasar Japan da ba ta da irin wadannan makamashi. Abu ne sananne cewa wanda duk ya ke rike da albarkatun kasa, ya na rike da duniya. Ko da a fannin kirkire-kirkire, ko fannonin kimiyya da fasahohi, ko bunkasar fasahohi, ba za a iya raba su da bukatuwa zuwa ga albarkatun kasa ba. Abu ne a fili cewa kasar Amurka ta gudanar da yaki a Gabas ta Tsakiya ne, sabo da yankin yana da albarkatu. Sabo da haka ina ganin cewa, kasashen BRICS za su iya samun wata kyakkyawar makoma, wajen samun bunkasuwa a nan gaba." (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China