Wakilin majalisar gudanarwar kasar Sin Yang Jiechi, da kuma manyan wakilan kasashen Afirka ta Kudu, da Brazil, da Rasha, da Indiya sun halarci taron.
Kafin fara taron, mahalartansa sun yi shiru na dan wani lokaci, domin nuna jimaminsu ga rasuwar tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu Nelson Mandela.
Shi ma a jawabinsa ga mahalarta taron, Mr. Yang Jiechi ya gabatar da sakon ta'aziyya a madadin kasar Sin, ga 'yan uwa da kuma al'ummar Afirka ta Kudun.
Don gane da harkokin kungiyar ta BRICS kuwa, Mr. Yang ya bayyana cewa, kamata ya yi kasashe biyar mambobin kungiyar su aiwatar da manufofin da suka cimma ra'ayi daya a kansu, yayin ganawar da ta gabata a birnin Durban, su kuma karfafa hadin gwiwarsu a fagen inganta sabbin ra'ayoyin tsaro da fahimtar juna, amincewa da juna, yin zaman daidai wa daida da cimma moriyar juna.
Har ila yau wakilin na kasar Sin ya ce, abu ne da ya dace ga kasashensu su goyi bayan aikin tsara ka'idojin kasashen duniya, da kiyaye tsaron kasa da kasa, da na shiyya-shiyya, tare da kara yin mu'ammala kan harkokin inganta bunkasuwa da yanayin tsaro, ta yadda za a iya karfafa hadin gwiwa yadda ya kamata, a fannin tsaro bisa manyan tsare-tsare. (Maryam)