Ma, wanda ya yi wannan tsokaci yayin taron 'yan jaridu na gida da na waje, ya bayyana cewa, za a gudanar da taron birnin Durban a ranar 26 da 27 ga wata. Yanzu kasashen BRICS suna yin shawarwari kan batun kafa asusun musayar kudaden kasashen waje, yayin da hukumomin kudi na wadannan kasashe suke nazari kan hakikanin abubuwa da suka shafi wannan batu.
Yayin dai wannan taro, shima mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin, Zhai Jun ya bayyana cewa, za a yi taron yin shawarwari tsakanin shugabannin kasashen BRICS da na kasashen Afirka a yayin taron na Durban dake tafe. Ana fatan dai wannan taro zai karfafa shawarwari, da hadin gwiwa tsakanin kasashen BRICS da na nahiyar Afirka, tare da kara karfin wakilci na kasashe masu karfin bunkasar tattalin arziki, da kasashe masu tasowa cikin harkokin duniya. (Fatima)