in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Palesdinu ta nemi Amurka ta sa hannu don kada rikici a tsakanin Palesdinu da Isra'ila ya kara tsananta
2014-07-01 15:56:05 cri

A ranar Litinin, wani jami'in Palesdinu ya ce, shugaban al'ummar Palesdinu Mahmoud Abbas ya bukaci kasar Amurka da ta sa hannu don kada rikicin soja a tsakanin Palesdinu da Isra'ila ya kara tsananta sakamakon kisan gillar da aka yi wa wassu 'yan mata matasa Yahudawa 3 da suka bace.

Wannan babban jami'in Palesdinu da ba ya son bayyana sunansa ya tabbatar a wannan rana da cewa, Abbas ya yi zargin cewa, Isra'ila tana son habaka tasirin lamarin fiye da kima, tana kuma son yin amfani da wannan hujja, domin kara daukar matakan soja a gabar yamma ta kogin Jordan da zirin Gaza, ta yadda za ta lalata yunkurin shimfida zaman lafiya a tsakanin sassan biyu. Jami'in ya jaddada cewa, Abbas ya kai suka kan lamarin kisan gillar 'yan matan matasa Yahudawa 3, tare da nanata cewa, har kullum Palesdinu bata amince da ko wane irin aikin nuna karfin tuwo ba.

A nasa bangare, firaministan kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi nuni da cewa, ya kamata kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas ta biya diyya ga iyalan wadanda aka yi ma kisan gillar guda 3.Sai dai kakakin kungiyar Hamas Abu Zuhri ya musunta zargin da Isra'ila ta yi mata, yana mai cewa babu wata kungiya a Palesdinu da ta sanar da daukar nauyin aikata wannan danyen aiki, kana dalilin da ya sa Isra'ila ta sanya wannan laifi a kan Hamas shi ne, domin tana son kara daukar matakan soja kan Palasdinawa da Hamas. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China