in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fatah da Hamas sun cimma daidaito kan membobin hadaddiyar gwamnatin Palesdinu
2014-05-28 15:38:25 cri
Manyan kungiyoyin siyasa biyu na Palesdinu wato Fatah da Hamas sun cimma daidaito kan jerin sunayen membobin hadaddiyar gwamnatin kasar a ranar 27 ga wata, kuma za a gabatar da jerin suneyen na karshe a ranar 29 ga wata. Hadaddiyar gwamnatin kasar mai kunshe da wakilan sassan biyu za ta fara aiki ne a wannan mako, ya zuwa watanni 6 kafin babban zaben kasar.

Bayan cimma yarjejeniyar neman sulhuntawa ta Palesdinu, Isra'ila ta sanar da dakatar da yin shawarwari da wakilan Palasdinawa. Isra'ila ta bayyana cewa, Hamas tana kokarin halaka Isra'ila, don haka ba za ta yi shawarwari tare da gwamnatin Palesdinu dake kunshe da membobin Hamas ba. Yanzu dai, an dakatar da yin shawarwari a tsakanin Palesdinu da Isra'ila, amma bangarorin biyu sun bayyana cewa, za su yi kokarin sake yin shawarwari bisa sharadi mai dacewa. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China