Sojojin gwamnatin kasar Iraki dai sun ci gaba da yin musayar wuta da dakarun 'yan adawa a jihar Diyala a ranar 30 ga watan Yuni, haka kuma an ci gaba da fafatawa a birnin Tikriti dake jihar Salah od Din. Wani hafsan sojojin gwamnati ya bayyana cewa, sojojin sun kwace kofar yamma ta birnin Tikriti, kafin daga bisani su kara kwace kofar kudancin birnin.
A daya bangaren kuwa, tashe-tashen hankula a kasar Irakin, sun tilasawa ma'aikata fiye da 1200 na kamfanin CMEC na kasar Sin dake aiki a birnin Samarra a dab da yanki mai fama da rikicin kauracewa wuraren aikinsu. A karkashin kokarin Sin da Iraki, an kai wadannan ma'aikata birnin Baghdad, kafin jigilarsu zuwa kasar Sin. (Zainab)