in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An ci gaba da dauki-ba-dadi a kasar Iraki
2014-06-30 14:19:15 cri

Bisa labarin da sojojin kasar Iraki suka bayar a ranar 29 ga wata, an ce, sojojin gwamnati da dakaru 'yan adawa sun ci gaba da fafatawa a jihohi daban daban na kasar. Inda a daren ranar Asabar ma, jiragen saman soja biyar da kasar Iraki ta sayo daga kasar Rasha sun isa birnin Baghdad.

Wani jami'in hukumar 'yan sanda na jihar Salah od Din ya bayyana cewa, tun daga ranar 28 ga wata, sojojin gwamnatin kasar masu tarin yawa sun nufi birnin Tikriti da dakarun ISIS ke iko da shi domin kwato shi.

Har wa yau, kakakin firaministan kasar Qassim al-Moussawi ya bayyanawa taron manema labaru cewa, kawo yanzu sojojin gwamnatin kasar sun kwace jami'ar Tikriti.

Ma'aikatar tsaron kasar Iraki ta bayyana a ranar 29 ga wata cewa, jiragen saman soja 5 da ma'aikatar ta saya daga kasar Rasha sun isa kasar, kuma sojojin saman kasar za su fara amfani da su ba tare da bata lokaci ba. Matakin da zai taimakawa sojojin gwamnati wajen kai hari kan dakarun 'yan aware ta sama.

A hannu guda kuma, babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya bayar da wata sanarwa ta kakakinsa a ranar 29 ga wata, inda ya nuna damuwa ga tsanancin hali da kasar Iraki ke ciki, da karuwar yawan fararen hula da suke rasa rayukansu sakamakon rikice-rikice, da rasa gidaje da mutane fiye da miliyan 1 suka yi a sassan kasar. Kana Ban ya yi kira ga bangarori daban daban da abin ya shafa da su dakatar da kisan fararen hula, ya kuma kalubalanci gwamnatin kasar da ta gurfanar da sojoji masu saba dokar jin kai ta duniya da dokar kare hakkin dan Adam a gaban kotu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China