in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gaza zabar sabon shugaban majalisar dokokin kasar Iraki
2014-07-02 14:43:17 cri
An gudanar da zaman farko na sabuwar majalisar dokokin jama'ar kasar Iraki a jiya Talata, koda yake an gaza zabar sabon shugaban majalisar.

Da safiyar ranar Talatar ne dai, sabbin membobin majalisar dokokin jama'ar kasar Iraki 328 suka halarci zaman, inda suka tattauna kan zaben sabon shugaban majalisar da mataimakan shugaban majalisar guda biyu, amma ba su cimma daidaito ba. Mukaddashin shugaban majalisar Mahdi al-Hafidh wanda ya jagoranci zaman ya bukaci mahalartansa su huta na dan lokaci kafin a ci gaba, sai dai wasu mahalartar taron sun yi tafiyarsu, don haka ba a samu cikakken adadin mutane da za su karasa zaman ba. Don haka, al-Hafidh ya sanar da dakatar da taron, kana ya ce, da zarar jam'iyyun siyasa daban daban na kasar suka kai ga cimma daidaito a cikin mako daya, za a ci gaba da gudanar da zaman a ranar 8 ga wata.

An gudanar da zaben majalisar dokokin jama'ar kasar Iraki ne dai a ranar 30 ga watan Afrilu, kuma hukumar koli ta zaben kasar ta sanar da sakamakon zaben a ranar 19 ga watan Mayu. Kafin daga bisani, babban kotun kasar ta amince da sakamakon a ranar 16 ga watan Yuni. Bisa kundin tsarin mulkin kasar Iraki, bayan da aka amince da sakamakon zaben, tilas ne a gudanar da taron sabuwar majalisar a cikin kwanaki 15 don zabar sabon shugaba da mataimakan shugaban majalisar. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China