Gwamnatin kasar Sin ta tsai da kudurin sake bude ofishin jakadancinta a kasar Somaliya, za ta kuma tura wata tawaga zuwa Somaliya a ranar 1 ga watan Yuli domin gudanar da ayyukan sake bude ofishin jakadancin, kamar yadda kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya sanar a yau Litinin ranar 30 ga wata a nan Beijing.
Hong Lei ya kara da cewa, kudurin da gwamnatin Sin ta tsai da ya nuna cewa, kasar Sin na sa muhimmanci kan raya dangantaka a tsakaninta da Somaliya, tana kuma mara wa Somaliya baya wajen sake gina kasar. Kasar Sin za ta yi amfani da damar maido da ofishin jakadancinta a Somaliya wajen inganta hadin gwiwa da abokantaka a tsakaninta da Somaliya a fannoni daban daban, a kokarin bude sabon shafi na bunkasa huldar da ke tsakanin Sin da Somaliya da kuma ba da gudummowa wajen wanzar da dawaumammen zaman lafiya a Somaliya da sake gina kasar. (Tasallah)