Rahotanni na cewa, a halin yanzu, akwai sojojin kasar ta Jamus da ba sa shiga fagen yaki a kasar Mali, inda suke taimaka wa kasar Mali wajen horas da rundunonin sojojin kasar. Sojojin da kasar Jamus za ta tura zuwa kasar Mali a wannan karo za su gudanar da aikin kare filin jirgin sama na Bamako ne.
A sa'i daya kuma, gwamnatin kasar Jamus na shirin tura karin sojojin sama zuwa kasar Afirka ta Tsakiya, don samar da taimakon sufuri da kuma kara mai ga jiragen sama cikin sama ga kungiyar tarayyar kasashen Turai, yayin da ta dauki matakan sojanta a kasar Afirka ta Tsakiya. Kuma a ran 20 ga wata kungiyar ministocin harkokin wajen kungiyar EU za ta tsai da shawara kan shirin daukar matakan soja a kasar Afirka ta Tsakiya. (Maryam)