Da dama daga masharhanta dai na ganin Markel za ta yi amfani da ziyarar ta ta a wannan karo wajen kara bunkasa wannan dangantaka, yayin da kuma za a baiwa batun bunkasar tattalin arziki muhimmacin gaske.
Wani ma jawabi da aka fitar ta tashar yanar gizon DW, ya nuna cewa madam Merkel ta fi zantawa da mahukuntan kasar Sin, sama da ragowar kusoshin kasashen Turai.
A kuma ziyarar ta wannan karo, Merkel da za tatake jagoranci jagorantar wata tawagar manayan wakilan kamfanoni, za ta mai da hankali sosai wajen gudanar da shawarwari game da bunkasar tattalin arziki. Kaza lika wannan kafar yada labarai ta kara da cewa, kasar Sin na taka rawar gani wajen bunkasar tattalin arzikin Jamus.
A halin da ake ciki dai kasar Amurka ce kadai kasa guda, da Jamus ke mu'amala da ita sama da Sin a fannin tattalin arziki. Inda a cikin shekaru sama da 10 da suka gabata, kamfanonin Jamus da dama suka ci gajiyar saurin bunkasuwar tattalin arzikin Sin, musamman ma a fannonin da suka shafi kera motoci, da kere-keren na'urori. Matakin da kasar ta Jamus ke matukar kokarin kiyaye yadda ya kamata.(fatima)