in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fatah da Hamas sun daddale yarjejeniyar sulhu
2014-04-25 20:47:38 cri

Shugaban al'ummar Palesdinu Mohmoud Abbas, ya bayyana cewa, Kungiyar 'yantar da al'ummar Palesdinu ta Fatah da yake shugabanta, da kuma Kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas, da ke da iko da zirin Gaza, sun amince da wata yarjejeniyar sulhunta tsakanin su.

Har wa yau kungiyoyin biyu sun yarda da kafa gwamnatin hadin gwiwa nan da makonni 5 masu zuwa, tare da gudanar da babban zaben kasa bayan watanni 6 da kafuwar gwamnatin hadin gwiwar.

Game da hakan, ofishin firaministan kasar Isra'ila ya bayar da wata sanarwa a daren ranar Laraba, inda ya ce Israila ta amince da jingine shawarwarin da aka yi shirin gudanarwa a wannan rana tsakanin ta da Palesdinu .

Kaza lika kakakin majalisar gudanarwa ta kasar Amurka Madam Jen Psaki, ta bayyana a gun wani taron manema labaru a wannan rana, cewa Amurka ta yi takaicin daukar wannan mataki na hadewar Fatah da Hamas. Daga nan sai Psaki ta sake nanata matsayin Amurka kan wannan batu, wato tilas ne ko wace irin gwamnati ta Palesdinawa ta yi alkawari a fili cewa, za ta kauracewa amfani da karfin tuwo, tare da amincewa da kasancewar kasar Isra'ila, tare da bin yarjejeniyoyin da bangarori daban daban suka daddale kan hakan. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China