in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Falasdinu ta aike da bukatar neman shiga yarjeniyoyin MDD
2014-04-03 11:21:58 cri
Wakilin al'ummar Falasdinawa a MDD Riyad Masour, ya ce Falasdinu ta aike da sakon neman shiga yarjeniyoyin MDD a ranar Talata, bayan da mahukuntan Isra'ila suka ki amincewa su saki fursunoni Falasdinawa da suke tsare da su, kamar yadda shirin farfado da zaman lafiya tsakanin sassan biyu ya tanada.

A baya dai an shirya bangarorin biyu za su yi musayar fursunoni 104, karkashin yarjejeniyar da Amurka ke sanyawa ido.

Masour ya ce Falasdinu ta yanke shawarar gabatar da wannan sabuwar bukata ga MDD ne bisa burinta na kare martaba da hakkokin al'ummarta. Wakilin al'ummar Falasdinun ya kuma kara da cewa, Falasdinawa na fatan za a kai ga samun hanyar aiwatar da shawarwari managarta kafin kai wa karshen wa'adin yarjejeniyar tsagaita bude wuta dake tafe nan da ranar 29 ga watan nan na Afirilu.

Ya ce babban burin da aka sanya gaba, bai wuce daukar matakan cimma matsaya guda ba, don gane da kudurin wanzar da zaman lafiya mai dorewa tsakanin sasssan biyu.

Da yake tsokaci don gane da wannan batu, mataimakin kakakin MDD Farhan Haq, ya tabbatar da samun sako na Falasdinu. Ya kuma ce MDD za ta duba wannan bukata da kyau domin daukar mataki na gaba.

Wasikar da Falasdinun ta gabatar dai na kunshe da bukatar shiga yarjeniyoyin dake baiwa yara, da mata, da raunana, da ma ragowar fararen hula kariya, daga cin zarafi da keta hakkokinsu a yayin tashe-tashen hankula ko yaki. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China