in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Palesdinu ta sanar da burinta na shiga cikin hukumomin MDD
2014-04-02 11:06:58 cri

Shugaban kasar Palesdinu Mahmoud Abbas ya sanar a ranar 1 ga watan Afrilu da cewa, kasar za ta sake kaddamar da shirin neman shiga cikin hukumomin MDD da yarjejeniyoyin duniya, wanda aka dakatar da shi a cikin watanni 8 da suka gabata, Abbas ya ce, Palesdinu ta yi hakan ne domin mayar da martani ga Isra'ila, wadda ta ki yarda da aiwatar da yarjejeniyar sako da Palasdinawan da take tsare da su a karon karshe.

Abbas ya bayyana hakan a gun bikin sanya hannu kan takardar neman shiga cikin hukumomin MDD a ranar da dare tare da sanar da cewa, nan take Palesdinu za ta gabatar da takardun neman shiga cikin hukumomin MDD da yarjejeniyoyin duniya guda 15. Ya ce, idan a karshe dai Isra'ila ta ki sakin Palasdinawan karshe da take tsare da su, to, Palasdinu za ta nemi shiga cikin dukkan hukumomin MDD da yarjejeniyoyin duniya guda 63.

A sa'i daya kuma, Abbas ya karfafa cewa, sake kaddamar da shirin, 'yanci ne da Palesdinu take da shi, haka kuma, bai tabo batun janyewar Palesdinu daga shawarwarin shimfida zaman lafiya ba.

An ce, takardun da aka sa hannu a wannan karo ba su kunshe da takardar neman shiga cikin kotun hukunta laifuffukan duniya . (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China