Bisa labarin da aka bayar, an ce, ya zuwa yanzu, yawan mutane da suka mutu a sakamakon fashewar bom din ya kai 14, kana mutane 26 sun ji rauni.
Fashewar bom din ta faru a ranar 17 ga wata da misalin karfe 8 da minti 15 da dare, yayin da jama'a suke kallon gasar cin kofin duniya a tsakanin Brazil da Mexico. Wani mutum da lamarin ya faru gabansa ya bayyana cewa, an dana bom din a kan wani babur mai tayoyi 3, karfin tashin bom din ya lalata gine-ginen dake dab da wurin.
A nasu bangare 'yan wasan kungiyar kasar Nijeriya dake halartar gasar cin kofin duniya a kasar Brazil sun yi allah wadai da lamarin. Emmanuel Attah, wani jami'in kungiyar ya bayyana cewa, 'yan wasan za su kara yin hadin kai da kokarin samun sakamako mai kyau don jajantawa masu sha'awar wasan a cikin gida. (Zainab)