A Jiya Jumma'a ne aka gudanar da gasar "rera wakokin Sin tsakanin dalibai 'yan Najeriya".
An gabatar da wannan gasa irinta ta farko ne a kwalejin Confucius dake jami'ar Lagos dake tarayyar Najeriya. Inda dalibai kimanin 200 ciki hadda 'yan ajin manya na kwalejin Confucius, da na cibiyar koyar da Sinanci ta kwalejin Confucius suka fafata cikin gasar.