An dai nada sabon sarkin ne kwanaki biyu da rasuwar marigayi Alh. Ado Bayero, wanda a ranar juma`ar nan ne ya cika mako guda da rasuwa, amma wasu dalilai suka haramtawa sabon sarkin shiga fada kamar yadda al`ada ta tanada.
Girke jami`an soji da `yan sanda bisa umarnin gwamanatin tarayya a harabar fadar, na daga cikin dalilan da suka dakatar da sarkin shiga fadar, amma duk da haka ya samu mallakar mahimmai daga cikin kayan nadin sarauta, wadanda suka hadar da hular Azurfa, da takalmin gashin Jimina da kuma tagwayen masu, bayan da gwamnan Kano ya damka masa takardar shaidar kama aiki.
Sabon sarkin ya shiga fada ne da misalin karfe hudu na yamma, ta wata sabuwar kofa da aka sara masa a jikin katangar gidan sarki, kamar yadda al`adar gidan sarautar kano ta tanada.
Malam Sunusi Lamido Sunusi ya kasance sanye da fararen kaya, sannan kuma ya hau wani farin doki bisa rakiyar daruruwan jama`a a yayin shigar sa gidan.
Kafin shigar sa fadar, sai da ya jagorancin sallar juma`a, a masallacin juma`a na gidan gwamnatin kano, inda aka gudanar da addu`oi na neman gafara ga marigayi Alhaji Ado bayero.
Yanzu dai komai ya lafa a jihar kano, bayan tarzomar data afku a makon jiya jim kadan da sanar da nadin sabon sarkin.(Garba Abdullahi Bagwai)