Kaba na mai ci gaba da cewa, Kwadibwa na da albarka da kuma babban buri. To amma ta ce, wannan buri na bukatar kudade, ka'idoji da bankin shige da fice na kasar Sin (Exim) ya bayar sun dace.
Ta ce, tana ganin rance da bankin Exim na kasar Sin zai bayar za'a yi amfani da su a wasu ayyuka na gaggawa, kuma ya dace kasar ta Kwadibwa ta kammala zuba jari a fuskar ababan rayuwa domin ci gaba mai dorewa.
Ta kara da cewa, kudin ruwan na bashin ba su da yawa, kuma akwai tsawon lokaci na biyan bashi, ban da wannan kuma akwai karin lokaci idan an samu jinkiri na shekaru 7 zuwa 9.
Kasar Kwadibwa na ci gaba da shawo kan kalubale da suka taso sakamakon rikicin bayan zabe, wanda ya kawo cikas ga sassan tattalin arziki da dama a kasar.
Wani shirin gina kasa na da burin zuba jarin dalar Amurka biliyan 20 a shekaru 5 masu zuwa.
Domin kammala wadannan ayyuka, musamman ma a fuskar samar da ababan more rayuwa, kasar ta yammacin Afirka tana dogaro da masu bada tallafi da kasashe kawayenta.(Lami Ali)