A safiyar wannan rana, mutanen sun taru a gaban hukumar yanke shari'a ta yankin Prado. Wasu masu zanga-zanga sun sa rigar da aka rubuta "Mutumin da a kaiwa lahani bayan babban zabe", wasu kuma sun daga kyalaye da aka rubuta kalmomi cewa, "Ko kotun manyan laiffukan duniya tana cin hanci da rashawa?", "Kotun manyan laiffukan duniya, ko za mu iya amincewa da ke?", "Ko za a daidaita batun Gbagbo a siyasance?" da dai makamantansu.
A ran 3 ga wata, alkalan kotun manyan laiffukan duniya sun bayyana cewa, shaidun da masu gabatar da kararraki suka bayar ba su isa ba wajen yanke hukunci ga Laurent Gbagbo. Shi ya sa suka bukaci a kara ba da shaida ko kara yin bincike kan wannan batu.(Fatima)