Bisa labarin da muka samu, an ce, a shekarar nan ta 2014, kasar Sin za ta kebe kudin Sin har Yuan biliyan 1.28 ga aikin gona, kudaden da za a yi amfani da su wajen gudanar da ayyukan gwaje-gwaje 265, a fannoni biyu.
Fanni na farko shi ne na ayyukan shirin inganta manyan nagartattun kamfanoni, wadanda suke taimakawa sauran kamfanonin aikin gona. Irin wadannan kamfanoni da yawansu ya kai 108, za a ba su kudin Sin har Yuan miliyan 668.
A fanni na biyu kuma, wato fannin ayyukan da ke cikin shirin 'abubuwan musamman na ko wace gunduma', wadanda suka kai 157, an ware kudin Sin Yuan miliyan 612. Kasar Sin za ta dora muhimmanci ga taimakawa sansanin dashen itatuwa da kiwon dabobbi, da sarrafa amfanin gona, da kasuwannin sayar da kayayyakin gona masu yawan gaske, da kafuwar sansanonin ajiyewa, da na kiyaye danyun amfanin gona da dai sauransu.(Danladi)