Wani jami'in hukumar Arthur Tuda ya bayyanawa manema labaru cewa, bisa binciken da aka yi kan launi da girman wadannan hauren giwaye, an gano cewa na giwaye ne irin na kasar Kongo Kinshasa, da Tanzaniya, da wurin yawon shakatawar Tsayo dake kasar Kenya da dai sauransu.
Mr. Tuda ya ce, an kasha giwayen da yawan su ya haura dari daya kafin tattara hauren giwaye mai wannan yawa.
Shi ma a nasa bangare babban jami'in rundunar 'yan sandan birnin Mombasa Geoffrey Mayek, cewa ya yi jami'an sa suna bincike kan wani mutum 'dan asalin kasar Kenya, da ake zargi da laifin fasa-kwaurin hauren giwayen, kana ana neman sauran mutanen da suka taimaka wajen aikata wannan laifin.
Rundunar 'yan sandan dai na zargin 'yan ta'adda, da tattara kudade ta hanyar fasa-kwaurin hauren giwaye a yankunan dake dab da tekun kasar ta Kenya. (Zainab)