Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying wanda ta bayana hakan yayin taron manema labarai a nan birnin Beijing, ta kuma mika sakon ta'aziyar kasar ta Sin ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su.
Ta ce kasar Sin za ta ci gaba da taimakawa kasar Kenya a kokarin da take yi na kiyaye tsaro da cikakkun yankunan kasar.
Rahotanni na nuna cewa, kimanin 'yan bindiga 50 ne dauke da abubuwan fashewa suka shiga kasuwar garin na Mpeketoni da ke yankin Lamu ranar Lahadi da dare inda suka rika kashe mutane ciki har da wani dan sanda.
Kungiyar Al-shabaab ta Somaliya dai ta dauki alhakin kai wannan hari wanda ta bayyana a matsayin daukar fansa kana abin da ta kira tura sojoji da Kenya ta yi zuwa Somaliya domin mara wa sojojin kasashen waje baya a yakin da suke yi da 'ya'yan kungiyar da ke da alaka da Al-Qeada. (Ibrahim)