in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar Al-Shabaab ta ayyana kai yaki a Kenya
2014-05-22 20:50:28 cri
Wani jigo a kungiyar Al-Shabaab ya ce kungiyar za ta canza takitin da take kai wa hari daga kasar Somaliya zuwa kasar Kenya inda mayakan kungiyar suke kaddamar da hare-hare.

Fuad Mohamed Khalaf shi ne ya bayyana hakan ta kafar rediyon da ke mara wa kungiyar baya inda ya yi kira ga mayakan kungiyar da ke da alaka da kungiyar Al-Qaeda, da su kara zafafa hare-haren su a kasar ta Kenya.

Mayakan na Al-Shabaab dai sun sha yin arangama da sojojin Kenya dake karkashin tsarin dakarun wanzar da zaman lafiya na AU(AMISON),tun lokacin da dakarun AMISON din suka fatattaki mayakan kungiyar daga galibin yankunan kudancin Somaliya.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China