Kenyatta ya bayyana cewa, yanzu haka gwamnatinsa ta fara sanya na'urorin ganin kwakwab a dukkan manyan birane da garuruwan kasar da kuma kan iyakokinta, baya ga motoci 1,200 da aka samar wa 'yan sandan kasar.
Shugaban ya kuma bayyana shirin gwamnati na bullo da wani tsarin adana muhimman bayanai a shekara mai zuwa, inda za a rika adana bayanan da suka shafi harkokin tsaro da na shigi da fice ta hanyar amfani da na'urori na zamani.
Ya ce, yanzu abin da kasar ta Kenya ta sanya a gaba, shi ne hadin kan kasa, ganin yadda 'yan ta'adda ke barazana ga rayuka, dukiyoyin jama'a da kuma kayayyakin tarihi. (Ibrahim)