Wani babban jami'i mai kula da 'yan sandan birnin Nairobi ya gaya ma manema labaru cewa, fashewar ababen guda 2 sun abku ne a wani yankin dake dab da babbar kasuwar Gikomba. A cewarsa tashin abun na farko ya faru a cikin wani karamin bas dake daukar fasinjoji 14, yayin da fashewa ta biyu ta faru a cikin kasuwar Gikomba. Jami'in ya kara da cewa ba a san dalilin fashewar ababen ba tukuna, amma 'yan sanda sun riga sun cafke mutum daya wanda ake tuhumarsa da hannu a cikin wannan lamarin.
Kasuwar Gikomba da aka samu fashewar ababen ita ce daya daga cikin manyan kasuwannin birnin Nairobi, kana an ta da wadannan abubuwa 2 ne a lokacin da ake samun cunkuson jama'a cikin kasuwar. (Bello Wang)