Shugaba Poroshenko wanda ya bayyana hakan a jiya Lahadi, ya yi wani taron tattaunawa tsakaninsa da bangarori uku da batun siyasar yankin gabashin kasar ya shafa don lalubo hanyar aiwatar da shirin wanzar da zaman lafiya a yankin.
Har wa yau shugaba Poroshenko ya jaddada cewa, abu mafi muhimmanci a hanlin yanzu shi ne, mayar da tsarin gudanarwa a yankin gabashin kasar ta Ukraine, tare da tabbatar da tsaron rayukan jama'ar kasar dake zaune a yankin.
A dai ranar ta Lahadi an yi wani babban gangami a filin 'yancin kai dake birnin Kiev, inda wakilan jama'a suka bayar da wata sanarwa, wanda suka bukaci majalisar dokokin kasar ta yanzu, da sabon shugaban kasar Poroshenko, su tabbatar da lokacin gudanar da zaben majalisar dokokin kasar ba tare da bata lokaci ba. Ban da wannan, sanarwar ta kuma bukaci majalisar dokokin kasar da ta aiwatar da tsarin raba kujerunta bisa yawan kuri'un da jam'iyyun kasar suka samu, da kuma fatan majalisar za ta rage yawan kuri'un da jam'iyyu ke samun iznin shiga majalisar da su, daga kashi 5 zuwa kashi 3 cikin dari, domin idan har aka ci gaba da bin ka'idar yanzu, kungiyar siyasa da mahalarta babban taron jama'ar da suka hallara a filin 'yancin kai, ba ta da damar shiga majalisar dokokin kasar. (Zainab)