Bisa sanarwar da ofishi mai magana da yawun babban sakataren MDD ya fitar, an ce Zhou Yiping ya fara aiki a matsayin darektan ofishin sa kaimi ga hadin gwiwa tsakanin Kudu da Kudu, wato kasashen da tattalin arzikinsu ke tasowa, karkashin laimar MDD, a shekarar 2004. Ya dade yana jagotantar aikin Majalisar a fannin inganta da daidaita tsarin hadin kai da ake yi tsakanin kasashe masu tasowa.
Sanarwar ta kara bayyana cikakken tarihin mista Zhou Yiping, ta ce an haife shi a shekarar 1955, wanda ya kammala karatu a jami'ar Fudan ta kasar Sin a shekarar 1977. Sa'an nan ya fara aiki a MDD a shekarar 1985. Daga 1997 zuwa 2004 ya taba zama mataimakin darektan hukumar inganta hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa, wadda daga bisani aka gyara sunanta zuwa ofishin inganta hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa na MDD.(Bello Wang)