in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na da karfin sarrafa samaniyar kasar, in ji kakakin ma'aikatar tsaron kasar
2013-11-27 17:16:17 cri

A yau Laraba 27 ga wata, kakakin ma'aikatar tsaron kasar Sin Geng Yansheng ya ba da amsa kan batun dake jawo hankalin mutane game da shigowar jiragen sama masu jefa boma-bomai biyu mai samfurin B-52 na sojojin kasar Amurka a sassan tsaron sararin samaniya na tekun Gabas na kasar Sin a kwanan baya.

A cewar Geng Yansheng, wadannan jiragen sama biyu sun yi zagaye a gabashin sassan tsaron sararin samaniya na tekun Gabas na kasar Sin da aka shata ne daga karfe 11 zuwa karfe 1 da mintoci 22 na yammacin ranar 26 ga wata. Hakan rundunar sojojin kasar Sin ta sa ido, kuma ta tantance yanayin jiragen saman.

Ban da haka, Mr Geng ya jaddada cewa, Sin ta tantance jiragen saman kasar Amurka bisa dokokin tantance jiragen sama a sassan tsaron da aka shata na sararin samaniya na tekun Gabas, wanda ya ba da izni wajen tantance ayyukan da ko wane irin jirgin sama zai yi cikin sassan, ban da haka, kasar Sin na da karfin sarrafa sararin samaniyar ta. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China