in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta gina tasha ta farko da ke iya motsi wadda za a yi amfani da ita don yin gwaji a teku mai zurfi
2013-11-04 16:27:30 cri

Kamfanin kere-keren jiragen ruwa na CSIC na kasar Sin ya bayar da wani labari a ran 3 ga wata cewa, tasha ta farko da ke iya motsi wadda za a yi amfani da ita don yin gwaji a teku mai zurfi ta kasar Sin, wadda kuma kamfanin yake daukar nauyin nazari da gina ta, an riga an kamala aikin hada shi, a nan gaba ba da dadewa ba tashar za ta shiga cikin ruwa don yin gwaji.

Tare da na'urar shiga teku mai zurfi da ke da mutum a ciki mai lambar 'Jiaolong', tasha ta farko wajen yin gwaji a teku mai zurfi, ana daukan dukkansu biyu a matsayin manyan makamai da kasar Sin take dauke da su don gano sirri a cikin teku mai zurfi. Mistan Weng Zhenping da ke kula da harkokin da abin ya shafa na kamfanin CSIC ya gabatar da cewa, yanzu ana daidaita tashar, wadda nauyin kayayyakin da ta dauka ya kai ton 35, kuma za ta iya aiki a karkashin teku daga awoyi 12 zuwa 18, kuma za ta iya daukar mutane 6. Bisa wani shirin da aka yi, za a fara gwaji ne a cikin tabki a nan gaba kadan.

Weng kuma ya yi bayanin cewa, a nan gaba kasar Sin za ta yi nazari da gina tashar da ke iya motsi bisa matsakaicin mataki wadda nauyin kayayyakin da ta dauka zai kai ton 300, haka kuma Sin za ta gina tashoshin da ke iya motsi a teku mai zurfi wadanda nauyin kayayyakin da suka dauka zai kai ton 1500 da 2500.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China