Wani dan jarida ya tambaya cewa, ranar 5 ga wata, a gun taron sauraron kara, mataimakin sakataren harkokin waje na Amurka, Daniel Russel ya bayyana cewa, Sin ta gwada iko da moriyarta a yankin teku bisa layin iyakar kasar a tekun Kudu, wannan bai dace da dokokin kasa da kasa ba. Kamata ya yi a yi bayani kan wannan batu ko a kyautata matsayin kasar Sin. Game da wannan batu, mene ne ra'ayin kasar Sin?
Dangane da wannan, Hong Lei ya amsa cewa, game da rikici kan yankin teku tsakanin Sin da wasu sauran kasashe, Sin ta dade tana kokarin daidaita wannan batu ta hanyar yin shawarwari tsakaninta da kasashen da abin ya shafa kai tsaye. A sa'i daya, Sin tana dora muhimmanci kan tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan yankin teku ta hanyar tabbatar da 'sanarwar ayyukan kasashen dake yankin teku na Kudu' tare da kasashe membobin kungiyar ASEAN. Sin ta bayyana matsayinta a fili. Ta da zaune tsaye ba zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kudu maso gabashin Asiya ba. Maganar wasu jami'an Amurka a gun taron sauraron kara ba ta da ma'ana ko kadan.
Dadin dadawa, Hong ya kara da cewa, ana kalubalantar Amurka da ta bayyana ra'ayinta cikin adalci, domin taka rawar a zo a gani wajen tabbatar da zaman lafiya da bunkasuwa a wannan yanki.(Fatima)